Musulmi Fiye da Miliyan Biyu Suka Yi Aikin Hajin Bana

Alhazai

Musulmi fiye da milyan biyu ne suka hallara a kasar Saudi Arabia domin aikin hajjin bana. Yau ne ake hawan arafa a bana inda musulmi miliyan biyu zuwa uku suke hallara suna addu'o'i, da ibada.

Musulmi zasu yi dawafi suna kewaye Ka'aba, ginin da musulmi ko a ina a duniya suke fuskanta lokacinda suke sallah.

Hajji na daya daga cikin cikakan musulunci idan musulmi yana da hali akalla sau daya a rayuwarsa. Saura cikakan sun hada da imani da kadaicin Allah da Annabi Muhammadu a zaman manzo na karshe, da fidda zakka da kuma azumi cikin watan Ramadan da sallah lokaci biyar kowace rana.

Ga musulmi masu yawan zuwa hajji yana daga muhimman nasarori a rayuwarsu.

Hadarin kugiyar daukar kayan gine gine da ya auku a farkon watan nan a Ka'aba har mutane 109 suka halaka bai sa mahajatta sunyi kasa a guiwa ba.

Akalla wasu 400 suka jikkata.

A arfan ne Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yayi hudubarsa ta karshe shekaru dubu daya da dari hudu da suka wuce.