Musulmi a duk fadin duniya sun fara azumin watan Ramadan

Masallacin Alb Kosovo.

Al’ummar Musulmi a duk fadin duniya sun fara azumin watan Ramadan, wata mai tsarki a kalandar Islama.

Al’ummar Musulmi a duk fadin duniya sun fara azumin watan Ramadan, wata mai tsarki a kalandar Islama. Watan Ramadan shine wata na tara a kalandar Islama, ana kuma daukar azumi bayan ganin sabon wata. Azumin watan Ramadan ya sami asali ne shekaru dubu da dari hudu da suka shige lokacin da Musulmi suka hakikanta cewa an saukowa da annabi Muhammadu mai tsira da aminci alkur’ani mai girma. An bukaci Musulmi su yi azumi su kuma nisanta kansu daga shan taba ko jima’i daga safe zuwa faduwar rana. Wadansu suna amfani da wannan lokacin wajen sauya halaye da rayuwarsu.