Da sanyin safiyar yau lahadi, girgizar kasar data kai maki shidda da digo hudu ta girgiza arewa maso gabashin kasar Japan a yankin da mumunar girgizar kasar da kai maki 9.00 ta apku a farkon wannan shekara.
Babu dai wani rahoto da aka samu akan ko wasu sun jikatta ko kuma girgizar kasar tayi barna. Kamfanin wutar lantarkin kasar da girgizar kasar data auku a ranar sha daya ga watan Maris ta lalata, tace girgizar kasar ta yau bata yiwa kamfanin barna ba.
In dai ba’a mance ba fiye da mutane dubu maitan ne girgizar kasar data auku a watan maris ta kashe. Sa’anan kuma wasu mutum dubu tamanin ala tilas aka kwashe su daga gidajensu a saboda barazanar turiri mai guba daga masana’antar nukiliyan kasar