Musulmai Su Yawaita Salla Domin Falalar Kiyamun Laili

A yau dandalinVOA bakunci malam Abdulrazak Uba Musa malami a massalacin Usman Afnan, da ke gadon kaya, wanda ya bukaci al’umma musulmi da su jajirce a wannan wata domin gabatar da sallar dare ta kiyamunlaili domin ribarta ramadana da neman afuwa akan ayyukan asha da aka aikata.

Malam Abdulrazak, ya ce yana da kyau wajen yawaita ibada mussaman ma ta tsayuwar dare ba tare da ya sanya riya ko don ya ga wani yayi shima zai aikata ba, amma ana so yayi Ibada a son kansa ba don waninsa ya aikata ba.

Ya ce yawaita sallah dare ta kiyamunlaili lokacin da ake rubanya ayyukan al’ada kuma lokaci ne da ubanji ya ke cewa ina mai neman bukata ya zo na amsa masa – malam Abdulrazak ya ce a karshen dare ake so a fi jajircewa wajen ibada domin lokacin ne da mafi yawan mutane ke barci

Malam Abdul’rak ya ce ana so musulmi ya kauracewa aikata ayyukan ashsha, da kauracewa karya da gujewa duk wani abin da bai dace ba, ya kara da cewa ramadana ba lokaci bane da ya haramta hulda tsakanin ma’aurata, ta dalilin haka ne ya ja hankalin mata da cewar duk mu’amala tsakanin ma’aurta ba haramtacciya ba ce kafin lokacin daukar azumi.

ku bisauraricikakkiyar hirar mu da malam a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Musulmai Su Yawaita Salla Domin Falalar Kiyamun Laili