Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gudun Bada Na Buda Baki Ke Sa Samari Arcewa - Ra'ayoyin 'Yan Mata


A yau shirin namu na ramadana, bisa al’ada a wannan lokaci ne mafi yawancin samari ke kaiwa ‘yan mata kayan shan ruwa da kayan sallah a wani yunkuri na nuna soyayya da cika al’adar soyayya a watan ramadana.

A yau dandalinVOA ya waiwayi wannan batu ne na ko shin ‘yan mata sun fara samun kayan shan ruwa da na sallah, inda mafi yawansu ke cewa a wannan lokacin ne samari ke aran na kare sai kuma bayan azumi su lallabo suna neman shiri.

Wasu daga cikin ‘yan matan kamar yadda A’isha ta ce tuni saurayinta ya arce gudun kada ya bayar da kayan sallah, ko na shan ruwa kuma ta ce a nata ra’ayin duk saurayin da ya arce bai kawo kayan azumi ba lallai soyayyar sa ta kasance ba ta gaskiya bace.

Fatima, kuwa cewa ta yi tuni saurayinta ya kawo mata kayan shan ruwa kuma tana sa ran zai kawo mata kayan sallah a cewarta soyayyarsu bata karya ba ce kuma basa yaudara.

Mafi yawan ‘yan mata dai na cewa duk saurayin da bai kawowa budurwarsa kayan shan ruwa ba ko na azumi ba, bai kamata ‘yan mata su saurare su ba da zarar an kammala azumin watan ramadana.

Mun kuma ji ta baki samarin akan wannan dabi’a ta su ta gudu daga wajen ‘yan matan su, sai bayan ramadana ga kuma abinda suke cewa.

Mustapha Muhammad cewa ya yi tuni ya kai wa budurwarsa kayan shan ruwa saura kuma kayan sallah ya rage masa a cewarsa ko da ya gudu dole zai dawo hakan ce ta sa ya tsaya.

Ku saurari cikakkiyar hirar a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:22 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG