Jamia’an ‘yan sanda a jihar Chicago sun ce, harbe-harben da aka yi a wajen wani gidan jana’iza da ya jikkata mutane 15 a daren shekaran jiya Talata ya na da alaka da kungiyoyi masu tada kayar baya.
A wani taron manema labarai a jiya Laraba tare da magajin garin Chicago, Lori Lightfoot, da sauran wasu jami'an gwamnati, shugaban 'yan sandan bincike Brendan Deenihan ya ce, harbin na bindiga ya fara ne saboda rikicin da ke tsakanin wata kungiyar masu tada kayar baya da kuma membobin wata kungiya mai adawa da ita, yayin gudanar da jana'izar wani matashi da ke da alaka da kungiyar.
Jami’an ‘yan sanda sun ce, biyu daga cikin wadanda suka jikkata suna cikin mawuyacin hali.
Deenihan ya kuma ce, musayar wutar ta fara ne daga mutanen da ke wajen gidan jana'izar. Ya kara da cewa an kashe mutumin da ake jana'izar a makon da ya gabata, kuma an kashe shi ne domin ramuwar gayya.
Babban jami’in ‘yan sanda David Brown ya fada wa manema labarai cewa, akalla an gano harsasai 60 bayan harbe-harben duk da cewa akwai motocin ‘yan sanda biyu a wajen gidan jana’izar. Brown ya ce, wannan wani yanki ne da ke fama da matsalar tashe-tashen hankula a Chicago.