Inda shugabanin kungiyoyin al’umma da jami’an hukuma suka tantauna akan matsalolin tsaro a Nijar da makwaftanta da nufin bayar da shawarwarin da ka iya mafitar wannan al’amari.
A karshen wannan tantaunawar, daya daga cikin mahalarta, Jami’I a ofishin mai shiga tsakani na kasa Alhaji Moustapha Kadi ya ce irin wannan zama na da amfani.
Haka shi ma shugaban kungiyar makiyayan Arewacin jihar Tilabery Boubacar Diallo ya ce jin ra’oyoyin jama’a akan maudu’in da aka tantauna, abu ne da zai taimaka a sami mafita.
La’akari da irin gudunmowar da irin wannan shiri ka iya bayarwa wajen waye kan al’umma ya sa shugaban kungiyar AJEPA, Laouali Tsalha ya nuna bukatar ci gaba da tsara irin wannan haduwa ta musanyar ra’ayi.
A ci gaba da wannan rangadi Alhaji Aliyu Mustapaha ya gana da shugabanin wasu kafafen dake sha’awar kulla huldar aiki da Muryar Amurka wadanda suka hada da gidan radio da television labari da gidan radio da tv Dounia da Radio Wadata.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5