Najeriya: Taron Muryar Amurka Da Abokan Huldar Ta Daga Kasashen Yammacin Afirka

Taron Muryar Amurka a Abuja

Muryar Amurka tana gudanar da taro na kwanaki biyar domin tattaunawa da abokan huldar ta don samun kyakyawar fahimta game da irin shirye-shiryen da abokan huldar nata ke yadawa a tashoshin su.

Taron ya samu halartar shuwagabannin gidajen rediyo da talabijin daga kasashen Afirka kamar Nijar da Ghana da Togo da Senegal da kuma wasu daga jihohin Najeriya.

Mahalarta taron sun nuna jin dadin su game da taron, kuma sun bayyana irin tagomashin da suke samu da ga shirye-shiryen Muryar Amurka da suke yadawa a tashoshin su.

Har ila yau, wasu daga cikin mahalarta taron sun fadi wasu abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya tare da bada shawarwari.

Taron dai ya zama hanyar ganawa tsakanin masu aika rahotanni na VOA a Najeriya da shugabannin gidajen rediyon.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar.

Your browser doesn’t support HTML5

Muryar Amurka Na Gudanar Da Taron Tattaunawa Da Masu Aika Rahoto