Murnar Lashe Gasar Premier: Masoyan Liverpool Sun Rarraba Kayan Tallafi

  • Murtala Sanyinna

Magoya bayan Liverpool na rarraba tallafi

Masoyan Liverpool Sun Yi Murna Tare Da Rarraba Kayan Tallafi

Magoya bayan kungiyar kwallon kafar Liverpool ta Ingila a kasar Sudan ta Kudu, sun rarraba kayan abinci da sinadarin tsabtace hannu da sabulai da kuma takunkumin rufe baki da hanci, a yayin da suke bikin murnar nasarar lashe gasar Premier ta bana da kungiyar ta yi.

Magoya bayan Liverpool na rarraba tallafi

Kungiyar ta wallafa hotuna da dama a shafinta na twitter, wadanda kuma suka karade shafukan sada zumunta na internet, da ke nuna yadda suka rarraba kayayyakin ga masu manyan shekaru a garin Juba na kasar ta Sudan ta Kudu, a zaman wani sashe na tallafawa a lokacin annobar coronavirus.

“Dukan mu ‘yan uwa ne tsintsiya madaurinki daya” wani daga cikin gaggan magoya bayan kungiyar ta Liverpool da ya halarci rarraba tallafin John Mading Mabor ya wallafa a shafin na twitter.

Magoya bayan Liverpool na rarraba tallafi


Liverpool ta lashe gasar Premier ta bana, karo na farko a cikin shekaru 30, lamarin da ya sa masoyan kungiyar a duk fadin duniya suka shiga shagulgulan biki ta hanyoyi daban-daban.

Yanzu haka kuma kungiyar ce ke rike da kofin zakarun Turai, wanda ta lashe a kakar wasanni da ta gabata.