Muna Zaune Lafiya A Awka In Ji Hausawa

Mazauna Kudu Maso Gabashin Najeriya

Duk da rikicin da ya barke tsakanin wani manomi da Fulani makiyaya wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar manonin, alamuran na tafiya kamar yadda yakamata a jihar ta Anambra.

Bayan rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a garin Anaku, dake jihar Anambra yayi sanadiyar mutuwar mutun daya a makon da ya gabata. Al’umar jihar masamman Hausa mazauna Awka, babban birnin jihar, na cigaba da gudanar da harkokinsu hankali kwance.

Malam Adamu Datti, wani dan kasuwa mazaunin birnin Awka ne ya furta haka awani hira da wakilin muryar Amurka Alphonso’s Okoroigwe, yana mai cewa su dai kam suna zaune lafiya.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah, a yankin kudu maso gabashin Najeriya, Alhaji Gidado Siddiqi, yace kungiyar na kokarin gano wadanda suke da hannu a afkuwar wannan lamari kuma da sarar an gano su za a mika su ga hukuma.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Malam. Garba Umar, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin yace rundunarr na gudanar da bincike a kai domin gano makasudi abinda ya jawo faruwar rikicin.

Rikicin dai yayi sanadiyar mutuwar wani manomi ne mai suna Atuwanya, a yayinda da yake gonarsa lamarin da yasa ‘yan garin suka bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta magance mamayar makiyaya ko kuma su kare kansu a duk lokacin da irin wannan rikicvi ya taso.

Your browser doesn’t support HTML5

Muna Zaune Lafiya A Awka In Ji Hausawa -2'40"