Shin game da yaki da ta’addanci a Najeriya, akwai abinda hukumar take yi don ganin ta samar da wayewar kai ga mutanen kasa don gujewa fadawa cikin hadarin ‘yan ta’adda, kama daga kan tada bama-bamai ko kai hare-haren kunar bakin wake ta yadda mutane zasu ankare da duk wani motsin da bas u gane ba?
Wannan it ace tambayar da muka yiwa Dr. Garba Abari shugaban hukumar ta NOA a takaice. Inda kuma ya bayyana cewa suna iyakar kokarinsu don ganin sun wayar da kan jama’a ta hanyar amfani da radiyo, sakonin talbijin da ta hanyar maja’mi’u.
Shi kuma shugaban bangaren hulda da jama’a na hukumar sojin kasa ta Najeriya Birgadiya Janar Rabe Abubakar ya amsa mana yadda suke ta kokari ganin sun zage damtse da kuma bukatar ganin mutane sun basu hadin kan bankado bayanan da ka iya zama sanadiyyar murkushe hare-haren ta’addanci.
Ga cikakken sautin hirarsu a kasa don sauraro.
Your browser doesn’t support HTML5