Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar BJP Ta Indiya Ta Ci Garin Uttah Pradesh


 Fira-Ministan Indiya Narendra Modi
Fira-Ministan Indiya Narendra Modi

Jam’iyyar Firaministan Indiya Narendra Modi Bharatiya Janata Party wacce aka fi sani da BJP a takaice ta yi gagarumar nasara a Jihar da take da muhimmancin gaske a siyasance ta Uttar Pradesh.

Hakan ya baiwa Shugaban na Indiya karin karfin gwiwa kan mulkinsa har zuwa ragowar lokacinsa. Jihar da take da mafi yawan jama’a, inda jam’iyar ta BJP ta murkushe jam’iyyar da ke mulkin yankin Samajwadi Party. ita ce babbar kyauta ta zabe ga jihohi biyar da suka yi zaben jin ra’ayin a wannan makon.

Modi yace “ Ina mika godiya ga al’ummar Uttar Pradesh, wannan nasara mai dinbin tarihi ga BJP nasara ce ta samun ci gaba da kyakykyawar gwamnati”. Modi da kansa ya jagoranci yakin neman zabe a Uttar Pradesh, bayan alkawarinsa mai rikitarwa na haramta amfani da manyan takardun kudi.

Kudurin da da yawa suka ji tsoron zai ware masu zabe a jihohin da suke talakawa. Amma bayan bayyana goyon bayan shugaban na Indiya, Jam’iyyar BJP ta sami babbar nasarar da babu wata jam’iyya da ta samu irin ta cikin shekaru goma a jihohin da ake artabu akansu.

A cewar kwamitin zabe, tazarar ta haura yawan kujerun 'yan majalisu 320 a majalisar da ke da mazaunai guda 403.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG