Mun Gano Dala Biliyan 171 Da Babban Banki Ya Ki Shigarwa Asusun Gwamnati Daga Kudin Haraji - Kwamitin Bincike Na Shugaban Kasa

Sakataren kwamitin dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure

Wani kwamitin bincike na mutum 7 da shugaba Buhari ya kafa a asirce don duba ayyukan tara kudaden shiga na yau da kullum na bankuna, ya gano zunzurutun kudi da su ka kai dala biliyan 171 da babban bankin Najeriya ya ajiye a wani asusun da baya amfanar gwamnati.

Kwamitin ya ce kudin za su iya taimakon Najeriya ta rage jibgin bashin da a ke binta.

Mambobin kwamitin mai mutum 7 sun hada har da shugaban rundunar tsaron farin kaya DSS da tsohon kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Wakili.

Sakataren kwamitin dan majalisar wakilai Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana cewa sun yi tsayin daka har sai da gwamnan babban banki Godwin Emefiele ya bayyana gaban kwamitin, inda a ka ba da belinsa amma bincike na cigaba da gudana.

Gudaji Kazaure ya ce su na da cikekken goyon bayan shugaban kasa amma zuwa yanzu shi kansa ya kasa ganin shugaban don bayyana ma sa halin da a ke ciki.

Gwamnan babban banki Emefiele ya bayyana cewa na sa dalilan sauya fasalin kudin shi ne gano makudan kudin da ya dace su zauna a bankuna amma su na boye a hannun jama’a.

Emefiele ya ce fiye da Naira tirilyan 2.7 cikin Naira tirilyan 3.1 na hannun jama’a ne da wasu su ka boye.

Za a jira a ga yanda kwamitin zai yi bayan duba belin da ya ba wa gwamnan da kuma fatan ganawa da shugaba Buhari.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Mun Gano Dala Bilyan 171 Da Babban Banki Ya Ki Shigarwa Asusun Gwamnati Daga Kudin Haraji - Kwamitin Bincike Na Shugaban Kasa