Kungiyar matasan likitoci a Najeriya ta ce halin ko-in-kula da mahukunta su ka nuna game da sace abokiyar aikinsu Dakta Ganiyat Popoola ne ya sa su ka fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai daga jiya Litinin.
Sama da watanni bakwai kenan da sace Dakta Ganiyat Popoola da ke aiki a babban asibitin ido da ke Kaduna, amma har yanzu ta na hannun 'yan-bindigan daji wannan ne kuma ya sa kungiyar likitocin ta fara yajin aikin gargadi a kasar baki daya.
Tun bayan sace Dakta Ganiyat Popoola da mijinta da kuma wani dan 'yar uwarta aka yi ta fama da 'yan bindigan da su ka sace ta amma sai a watan Maris na wannan shekara su ka sako mijinta sannan su ka ci gaba da rike likitar da dan uwanta.
Kungiyar matasan likitoci reshen jahar Kaduna ta ce ganin halin ko-in-kula kan sako abokiyar aikin ta su duk da zanga-zangar da likitocin su ka yi ne ya sa aka fara wannan yajin aikin gargadi, inji sakataren kungiyar likitocin a jahar Kaduna, Dakta Yahaya Abdullahi.
Masana tsaro irin su manjo Yahaya Shinko mai ritaya na ganin wannan yajin aikin gargadi alama ce cewa harkar tsaro a Najeriya sai dai kowa tashi ta fishshe shi, inda ya buga misali da abun da ya faru da sarkin Gobir.
Ko kafin fara wannan yajin aikin gargadi dai akwai karancin likitoci a asibitocin wannan kasa saboda haka ne masu marasa lafiya a asibitoci su nuna damuwa masamman ganin karuwar marasa lafiya a asibitoci saboda yanayin damina.
Dakta Yahaya Abdullahi ya ce su na da bayanin halin da abokiyar aikin ta su ke ciki a hannun 'yan bindigan, shi ya sa su ka dauki wannan mataki.
A jiya Litinin dai rundunar 'yan-sandan Najeriya ta mika daliban koyan aikin likitanci 20 da ta ceto daga hannun 'yan-bindiga sannan ta sanar da kara a azama don ceto sauran al-umar dake hannun 'yan bindiga a sassan Najeriya daban-daban.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5