Cikin wadanda ke ficewar har da ‘yan takarar kujerar Gwamna da wasu ‘Yan Majalisar Dattawa dana Wakilai, lamarin da ya jawo gangami a Jalingo fadar jihar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu ‘yan takara da kuma wakilan zabe su kusan 400 suke haramar zuwa kotu bisa zargin cewa ba’a bassu sunyi zabe ba.
“Dalilan mu na zuwa kotu, don ba’a yi zabe ba. Mun zo da “delegates”, mu ‘yan takara munzo da su 16 akan za’a yi zabe. Ba’a yi zabe ba. Idan har basu tsaya sun dubi wannan abun da idon rahama ba, akwai dalilan, ko kuma hujjojin barin PDP”, a cewar Honorable Abacha dan takarar Majalisar Jiha ta Jalingo na daya.
To yayin da wasu ‘yan PDPn ke kokawa, wasu kuwa murna suke yi. Honorable Marafa Bashir Abba, shine aka baiwa takarar kujerar dan Majalisar Dattawa a mazabar Taraba ta Tsakiya.
“Mun godewa Allah, mun godewa jama’armu, da suka taru suka bamu goyon baya, ina so in tabbatar musu cewa zanyi musu aiki yadda suke bukata, kuma ina rokonsu, mu hada kanmu muyi babban zabe”.
Kamar Taraba, haka lamarin yake a Jihar Adamawa, inda anan ma wasu kusoshin Jam’iyyar ne da wasu ‘yan takara suke ficewa.
Alhaji Abdulrahman Kwachab na daga cikin wadanda suka fice daga PDP.
“Na farko abunda yasa, jam’iyyar PDP, mun bauta mata, mun raya ta, kuma muna kaunarta, shiyasa muka raya ta, dalilin da yasa muka rabu da wannan jam’iyya, rashin adalcinta, da cutar da ‘ya’yanta da take yi, munyi hakuri, munyi hakuri, hakurin ya kaimu makura, shiyasa dole ne, mu bar jam’iyyar, don masifa da bala’i da annoba.