Bayan kamala zaben, an bayyana sakamako har kowani dan takara ya ji adadin kuri’un da ya samu, to shi wanda ya lashe zaben tsohon Shugaban Kasa, Janar Muhammadu Buhari ya godewa jama’a duka, da suka bashi goyon baya har Allah Ya sa ya samu nasara a wannan zabe.
Janar Buhari yayi alkawarin cewa zai hada kai da ragowar ‘yan takarar su hudu, domin ciyar da Jam’iyyar APC gaba, kuma su ciyar da Najeriya gaba, da kuma yiwa jama’a aiki.
Tsohon shugaban ya bayyana cewa wannan nasara da ya samu, ba nasararshi bace shi kadai. Nasara ce ta jam’iyyar APC kuma nasara ce ta dukkan ‘yan Najeriya.
‘Yan takarar da basu samu nasara ba su hudu, sun amince da sakamakon zaben kamar yadda suka dauki alwashi tun farko, sannan zasu marawa Janar Buhari baya a yakin neman zabe da yake shirin farawa.
Sai dai Janar Buhari bai bayyana sunan mataimakinsa ba a wannan tafiya, inda zai yi karon battar karfe da shugaba mai ci yanzu, Goodluck Jonathan.
Ga sakamakon daga wakilin Muryar Amurka, Hassan Umaru Tambuwal.
Atiku Abubakar - 954
Muhammadu Buhari - 3430
Rabi'u Musa Kwankwaso - 974
Rochas Okorocha - 624
Sam Nda Isaah - 10
Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta kammala zaben fidda gwaninta, inda shugaba mai mulki Goodluck Jonathan ya karbi akalar takarar, tare da mataimakinshi Namadi Sambo.