An gano akwatin da ke dauke da na'urar tattara bayanan na jirgin da mai nadar magana, a cewar jami'an filin jirgin saman Kathmandu.
Hukumomin kasar sun ce ba a kai ga gano musabbabin hadarin jirgin mafi muni cikin shekaru talatin ba.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press, ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatan ceto sun yi awon gaba bincike wani wani kwazazzabo mai nisan mita 300 a kokarinsu na gano gawarwakin mutane. Jami’ai sun ce an gano akalla gawarwaki 68.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa AP cewa, “Gobarar ta yi zafi sosai, ta yadda ba za mu iya zuwa kusa da tarkacen jirgin ba. Na ji wani mutum yana kukan neman taimako, amma saboda harshen wuta da hayaki ba mu iya taimaka masa ba.”