‘Yan siyasa irinsu ministan cikin gida dan takarar jam’iyar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed na kan gaba a sahun wadanda suka ziyarci gidan Hama Amadou, domin ta ya shi juyayin rasuwar mahaifiyarsa kafin daga bisani sauran ministocin gwamnatin ta Nijer da ma ‘yan adawa su je.
Tun a yammacin Juma’ar da ta gabata ne ‘yan siyasa suka yiwa gidan shugaban na Moden Lumana Afrika ca da nufin taya shi juyayin rasuwar mahaifiyarsa wacce Allah ya yiwa cikawa a watan jiya a wani lokacin da yake gudun hijira a jamhuriyar Benin.
Ba’idin shugabannin jam’iyun adawa da suka je gidan na Hama Amadou domin yi masa gaisuwa, suma kusoshin gwamnati irinsu ministan cikin gida Bazoum Mohamed sun halarci wannan zaman makoki abin da ‘yan kasa ke ganinsa tamkar wani ci gaba a shirin warware takaddamar dake tsakanin bangarorin siyasar wannan kasa. Kabirou Issa na kungiyar DHD Afirka na da irin wannan ra’ayi.
An dade masu rajin kare dimokoradiya ke jan hankulan ‘yan siyasar Nijer akan bukatar jingine bambance banbamcen siyasa domin dorewar zaman lafiya a kasa.
Domin dorewar sabon yanayin dangantakar da aka shiga daga dawowar Hama Amadou gida kawo yau Abdou Elhadji Idi na hadakar kungoyin FSCN na mai shawartar ‘yan siyasa da magoya bayansu su yiwa juna adalci akan maganar tsare tsaren zabubukan dake tafe.
Tuni dai masu mu’amula da shafikan sada zumunta suka fara amfani da hotunan ziyarar da mukarraban gwamnati suka kaiwa jagoran ‘yan adawa da nufin fadakar da ‘yan kasa cewa siyasa ba batun kiyayya ba ne ballantana ta zama wata hanyar kulla gaba da abokin hamayya. Yayin da reshen jam’iyar Moden lumana a wata sanarwar ke jan hankulan magoya bayan wannan jam’iya cewa su kasance masu ladabi da biyayya kamar yadda shugabansu Hama Amadou ya umurcesu da shi.
Ga karin bayani cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5