Muhimmanci Da Illolin Amfani Da Hanyoyin Sadarwa Na Zamani

  • Saleh Shehu Ashaka

Wata mai kokarin buga waya.

Kazalika manyan 'yan siyasa, kan yi amfani da kafafen musamman Twitter wajen aikewa ga sakonninsu ga jama'a da magoya bayansu.

Muhimmancin sadarwar zamani irin su wayar salula, yanar gizo da tauraron dan adam ba za ta misaltu a takaitaccen bayani ba sai dai ba shakka hanyoyin aafanin da kafar yada labarai na dandalin musayar ra'ayi ta yanar gizo ka iya zama mai amfani ko aksain haka

Amfani ta fuskar fahimtar banbancin dabi'un mutane, sadar da sako ga shugabannin siyasa, furta albarkacin baki da sauran su. Sai dai illar ta shafi saurin yada labaran da ba su da tushe, yada kiyayya, tsiraici har ma ya da fasikanci.

'Yan Najeriya dai hazikai ne wajen amfani da dandalin Twitter, Facebook, 2go, Hi5 har ma da bude dadalin watsa labarai a yanar gizo kamar Gamji.com, dandalin siyasa, Dokin karfe da Sahara Reporters da ke watsa labarai daga Amurka.

Shugaban Mcathur Foundation Dr. Kole Shettima ya ce wata hanya ce da talakawa ka iya amfani da ita wajen aika sakonni ga shugabanni.

Aminu Baba Yaro Maude, daya daga cikin matasa 'yan siyasa da ke amfani da kafafen yada labarai na zamani kamar wasu da muka ji ra’ayoyinsu, suna ganin alherinsu wasu kuma na ganin akasin hakan.

Ba shakka wasu matasan kan yi amfani da kafafen ta hanyar da ba ta dace ba, kamar labarin wata matar aure da ta kama mijinta ya na daukar hoton al’aurarsa don aika wa wata abokiyar huldarsa a waje.

Haka kuma wasu mata ma na daukar tsiraicinsu ta wayoyin salula inda sukan aika wa samarinsu ta hakan, abin da ke nuna tabarbarewar tarbiyya.

Kazalika manyan 'yan siyasa, kan yi amfni da kafafen musamman Twitter wajen aikewa ga sakonninsu ga jama'a da magoya bayansu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Saleh Shehu Ashaka:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Mahimmanci Da Illolin Amfani Da Sadarwa Ta Zamani Ga Al’umma