A cikin jawabinsa na cikar shekaru 61 da samun ‘yancin kan Najeriya, shugaba Buhari ya ce gwamnati ta gudanar da cikakkiyar tattaunawa da kamfanin na Twitter inda kuma suka cimma matsaya da yarjejeniya.
Ya ce ana nan ana magance dukan matsalolin da aka bijiro da su a lokacin tattaunawar, don haka ya bayar da umarnin janye haramcin da aka yi kan amfani da kafar a kasar, idan har aka cimma sharudan da aka gindaya.
Sharudan ko sun hada da ba da damar yin amfani da shafin na Twitter ta kyakkyawar manufa, da kuma sharadin yin rijistar kamfanin a kasar.
Haka kuma an umarci kamfanin da ya rika biyan haraji, tare kuma da tsare wasu sharuda da suka danganci tsaron kasa, da kuma sanya ido akan sakwannin da ake wallafawa.
Gwamnatin Najeriya dai ta haramta amfani da shafin na Twitter a ranar 4 ga watan Yuni, bisa hujjar cewa ana amfani da kafar waje yunkurin wargaza kasar.
Sanarwar dakatar da Twitter din kuma ta zo ne jim kadan bayan da kafar ta shafe wani jawabin shugaba Buhari, da ya ke barazanar tunkarar masu fafutukar ballewa “da irin yaren da za su iya fahimta.”
To sai dai matakin ya fuskanci kakkausan suka daga ciki da wajen kasar, yayin da masu fashin baki kan tattalin arziki suka ce Najeriya na asarar kudin shiga Naira miliyan 103 a kowace sa’a ta dakatar da amfani da kafar.