YAMAI, JAMHURIYAR NIJAR - A zantawarsa da Muryar Amurka, inda ya yi Karin bayani kan muhimmancin wannan rana, Fasto Abdoulkader Korao na Church Eglise Assemblee de Dieu ta n’guwar Nouveau Marche dake birnin Yamai, y ace “Yesu Almasihu ya zo ya mutu an giciye shi duk da bai yi wani laifi ba. Saboda mu yam utu, kuma mutuwarsa ya dauki dukkan zunubanmu saboda mu samu fansa da ‘yanci. Ma’anar wanna rana Kenan, saboda mu samu bangaskiya a gareshi, mu kuma samu shiga mulkin Allah.
“An giciye Shi a ranar Juma’a amma a ranar Lahadi Ya tashi daga matattu”, in ji shi.
Ya kara da cewa duk da addu’o’I da ake yi a fadin majami’o’I, “kowane iyali na shirin da za su yi na wannan hidima ta Ista. Abunda zamu tunace kowani Kirista shine a kaucewa duk abun da zai samu cikin zunubi. Ku kuma shirya zukatanmu a gaban Ubangiji, mu samu sulhu da shi.
“Mu sami zaman lafiya, mu kuma kasance masu bada zaman lafiya”, a cewarsa.
Ranar Good Friday kokuma Vendredi Saint a Faransance na daga cikin mahimman ranakun shekara a wajen mabiya addinin Kirista abinda ya sa ake kiranta Juma’a mai mahimmanci
Ranar kan zama wata damar yawaita ibada domin neman albarkar ubangiji har ila yau.
Wani abinda ke kara fayyace mahimmancin wannan lokaci Kiristoci na darikar katolika a nasu bangare kan kammala azumin da suke gudanarwa a tsawon kwanaki 40 na kowace shekara.
Adamou Maidaji wani matsahin Kirista ne a majami’ar Eglise Evangelique na daukan wannan Juma’a ta good Friday da mahimmancin gaske.
A bana bukukuwan sallar Easter ko Pacques na zuwa a wani lokacin da Nijer da al’ummarta suka fuskanci kalubale da dama sakamakon hatsaniyar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Adamou Maidaji na Alfahari da tasirin addu’oi kan yanayi da aka shiga a kasar saboda haka za su kara azama akan irin wannan aiki.
Kamar yadda aka saba kristoci zasu hallara a majami’u domin raya dare a wannan Juma’a kafin su ci gaba da addu’oi a ranar Lahdin dake tafe yayinda ranar litinin 1 ga watan Afrilu wato ranar sallar Pacques kokuma Easter ke zama ranar hutu a wajen ma’aikata a hukumance.
A saurari cikakken rahoton Souley Moumoni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5