Muddassir Danladi Sidi: Ina Yin Rubutu Da Zai Amfani Al'umma

Muddassir Danladi Sidi

A shirin mu na Nishadi, VOA Haua ya samu hira da Muddasir Danladi Sidi matashi marubuci wanda ya samu nasara a wata gasar marubuta da aka gudanar a kasar Ghana.

Muddasir ya ce ya fara rubutu ne tun yana dan shekara 15, littafinsa na farko shine "Igiyar Allah," bayan ya kammala makarantar sakandare sai ya rubuta littafin da ake kira "Life Is Beautiful When The Heart Is Open" wanda yake bayani akan yadda rayuwa ta ke, mussaman a farkon rayuwar dan Adam.

Muddasir dai yana rubutu ne a harshen Turanci da Hausa sannan yakan rubuta littattafansa ne idan ya lura da wani batu da zai amfani al’umma.

Ga shi marubucin, ya karanci ilimin lissafi ne a jami'a wato Mathematics amma yake da sha'awar harkar rubutu.

Ya ce littafinsa na "Life Indeed", littafi ne da ya waiwayi rayuwar matasa, wanda da shi ne ya lashe gasar da ya samu nasara. Ya kara cewa littafin yana bayani ne yadda zaman banza yayi wa matasa katutu, da matsalolin da hakan yake haifarwa, da kuma hanyoyin da za’a bi wajen magance wadannan matsaloli.

Muddasir ya kara da cewa banda harkar fim, yana taba aikin jarida inda yake shirya fina-finai masu nisan zango na nishadi ko na ilmantarwa.

Haka kuma ya ce ya rubuta fina-finai kamar su 'Tunran Gini da Rumbun Dariya' da sauransu. Sannan ya kara da cewa baya fuskantar wata matsala sakamakon shi masani ne a fannin ilimin sadarwa na zamani.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

Muddassir Danladi Sidi: Ina Yin Rubutu Da Zai Amfani Al'umma