MTN Na Shirin Bullo Da Wayar Zamani Maras Amfani Da Katin Sim

MTN a Najeriya

Kamfanin sadarwar MTN a Najeriya ta fara gwajin amfani da wayoyin hannu marasa katin sim a wani kokarin jagorantar canjin da inganta kwarewar sadarwar zamani.

Wannan sabuwar hanyar kawo sauki a sadarwar zamani tana kunshe ne a wani mataki na gaba da zai ba wadanda suke da manyan wayoyi masu tsada su kai ga yin amfani da wayoyin su na hannu ba tare da abin da ake kira sim kad ba, wanda hakan yake nufin cewa za a iya amfani da layuka dayawa a waya daya ta yin amfani da lamba kawai.

Jami'in kula da fanin Kimiya da Fasaha a Kamfanin MTN Mohammed Auwal Abdullahi ya ce ilimi ne na cigaba a kimiyance wanda kuma zai kawo sauki wajen sadarwa da layuka iri daban daban a wayar hannu guda kuma zai hana yawan sace sace da ake yi ta hanyar amfani da sim kad.

A lokacin da yake bada bayanin wanan sabon salo, Injiniya Bako Wakil wanda shi ne mai kula da fanin Inganci da Nagarta na Hukumar Kula da Hanyoyin Sadarwa ta kasa, ya ce hukumar ta bada izinin a yi wanan gwaji na tsawon shekara daya domin a ga yadda zai taimaka wajen bunkasa hanyar sadarwar ba tare da yawan matsalolin da ake samu ba irin su sace sacen kudadaen mutane a banki da sace mutane a yi garkuwa da su da kuma sace wayoyi masu dauke da bayanan sirri na manyan jami'ai.

Ya ce wanan sabuwar hanaya za ta bada dama mutum ya yi mu'amala da mutane a ko ina suke a duniya ta yin amfani da lamba daya kawai.

Abin jira a gani shi ne ko wanan sabon salo zai kai ga kawo wa talaka sauki wajen sada zumunta da cutar Korona Bairus ta takaita.

Ga dai Medina Dauda Daga Abuja Najeriya:

Your browser doesn’t support HTML5

MTN ZATA KAWO SABON SALO