Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Aikawa Sarkin Saudiyya Wasikar Gaisuwa


Sarki Salman a lokacin da yake karanta wata takarda yayin taron koli na G20 wanda aka gudanar ta yanar gizo
Sarki Salman a lokacin da yake karanta wata takarda yayin taron koli na G20 wanda aka gudanar ta yanar gizo

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aikawa Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz da wasika bayan da aka kwantar da basaraken a asibiti.

"A madadina, da gwamnatina da kuma mutanen Najeriya, ina yi wa sarkin Saudiyya fatan warkewa cikin gaggawa. Sarki Salman ya kasance daya daga cikin shugabannin duniya mafiya inganci da na taba haduwa da su" in ji shugaba Buhari.

Buhari ya jaddada cewa "Sarki Salman babban aboki ne ga Najeriya kuma bai taba kin taimaka wa kasar ba a yayin lokacin bukata, saboda haka ina fatan ya samu sauki cikin gaggawa."

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannun kakakin fadarsa Malam Garba Shehu.

A safiyar yau ne kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya bayanna cewa an kwantar da sarkin a wani asibiti da ke Birnin Riyadh sanadiyyar fama da yake yi da matsalar mafitsara.

Haka ita ma Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa an kwantar da basaraken ne bisa matsalar mafitsara da yake fama da ita.

Tun shekarar 2015 sarkin mai shekaru 84 ya ke mulkin kasar ta Saudiyya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG