Mr P. Ya Nuna Fushinsa Kan Fadan Kabilancin Da Ya Faru a Ibadan

Peter Okoye (Mr. P Instagram)

Shahararren mawakin kudancin Najeriya Peter Okoye, wanda aka fi sani da Mr. P. ya nuna bacin ransa kan fadan kabilancin da ya faru a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Mr. P. ya nuna fushinsa ne a wani sakon Twitter da ya wallafa a ranar Lahadi inda ya ce ya zama dole a kawo karshen wannan nuna wariya da ake yi.

“Ya zama dole a kawo karshen wannan matsala ta nuna kabilanci da nuna wariya, Haba! Mene ne yake faruwa haka.” Mr. P. wanda a da yake waka da dan uwansa a P Square ya ce.

An samu rashin jituwa tsakanin matasan Yarbawa da na Hausawa a Sasha da ke birnin Ibadan a makon da ya gabata, lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi.

“Ni Igbo ne, matata Bayerabiya ce, a arewa na girma, a arewa na yi makaranta. Yau ina magana da harshen Hausa.” Mr. P. wanda aka haifa a birnin Jos na jihar Pilato da ke arewacin Najeriya ya kara da cewa.

A sakon nasa na Twitter, har ila yau mawakin ya yi amfani da wasu alamomi na emoji, wajen nuna bacin ransa kan abin da ke faruwa inda har ya saka maudu’in #StopThe BloodShed” – wato a dakatar da zub da jinin da ake yi.

Wannan rikici ya ja hankulan jama’a da dama musamman a arewacin Najeriya, lamarin da ya sa masu fada a ji suke ta kiran da a kai zuciya nesa.

Rikicin har ila yau ya sa hukumomin jihar sun saka dokar hana fita a yankin Akinyele da rikicin ya fi kamari.