Kasar Afirka ta kudu ta na shirin mika tsohon ministan kudin Mozambique, Manuel Chang, da gwamnatin kasar sa ba kasar Amurka ba. Kasar ta nema da a mika mata Chang saboda zargin aikata laifuka masu nasaba da kudi, a cewar wani jami’in Afrika ta kudu.
Chang, dan shekaru 63 da haihuwa an shirya sauraron shari'arsa a ranar Talata a Johannsburg. Yana tsare a gidan yari tun lokacin da aka kama shi a ranar 29 ga watan Disambar bara, yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa Dubai.
Kasar Amurka da Mozambique sun nemi a mika musu shi a kan zargin ya taka rawa a ciwo bashin dalar Amurka biliyan biyu ($2B) a asirce, badakalar data kusa jefa kasar Mozambique ta karye da kuma hada baki da akalla mutane goma sha takwas daga bangarorin biyu na kasashen.
Ministan harkokin Wajan Afrika ta Kudu, Lindiwe Sisulu, ta fada a wata hira da yayi da Jaridar kasar Daily Maverick wadda aka wallafa jiya Alhamis, cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ta amince ta mika Chang don ya fuskanci shari’a a Mozambique.