Monaco Ta Kai Karar Wasu Kungiyoyi Ga Humukmar FIFA

Kungiyar kwallon kafa ta Monaco, ta kai karar wasu kungiyoyin kwallon kafa ga hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, sakamakon kusantar dan wasan kungiyar Kyalian Mbappe, da kungiyoyin suka yi ta hanyar da bata dace ba.

Matashin ya kasance dan wasan da ya yi matukar farin jinni ga sauran kungiyoyi a kakar wasannin kwallon kafa ta bana.

Dan wasan mai shekaru 18, da haihuwa ya jefa kwallaye 27, ya kuma taimaka wajan bada kwallayen da aka jefa raga 17, a wasanni 59, a dukkan gasar wasannin yayin da taurariyar kungiyar Monaco, ta haska a wasan kusa da na kusa da na karshen kakar wasannin UEFA da ta gabata.

A kasance tare da mu domin karin bayani.