WASHINGTON D.C —
A wani rahoton da hukumar dake kula da kwallon kafa a nahiyar Afirka Confederation of African (CAF) ta fitar, ta ce tana shiri don ganin ta kara yawan kasashen da suke halartar gasar cin kofin kasashen Afirka (African Cup of Nation) daga kasashe 16 zuwa kasashe 24.
A cewar NFF, da ta rubuta a shafinta na yanar gizo ta bayyana cewa hukumar CAF, ta bayyana hakan ne a wani taro da ake yi na kwana biyu akan batun African football Symposium a kasar Morocco, ranar Talata 18/7/2017.
Taron ya samu halartar shugaban hukumar CAF Ahmad, da na FIFA Gianni Infantino da kuma Amaju Pinnick, na NFF ta Najeriya, da dai sauran shuwagabanin hukumar wasanni na kasashen Afirka.
Facebook Forum