Mohammed Salah Ya Kamu Da Coronavirus

Wani mai kaunar Bayan Mohammed Salah duke da hotonsa

Rahotanni daga kasar Masar na cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mohammed Salah ya kamu da cutar COVID-19.

Kungiyar kwallon kafar kasar ta Masar ce ta bayyana hakan a shafinta na Twitter inda ta ce dan wasan yana cikin koshin lafiya kuma bai nuna wasu alamun cutar ba.

Sanarwar ta kuma kara da cewa dan wasan zai kebe kansa.

Hakan na faruwa ne yayin da kungiyar Masar ke shirin karawa da Togo a wasannin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a birnin Alqahira.

“Sakamakon gwajin cutar coronavirus da kungiyar wasanmu ta gudanar, ya nuna cewa dan wasanmu Mohammed Salah, wanda dan wasan Liverpool ne, ya kamu da cutar coronavirus, ko da yake, ba ya nuna wasu alamun cutar.” Sanarwar ta ce cikin harshen larabci.

“Sakamakon gwajin sauran ‘yan wasan kungiyar ba sa dauke da cutar.” In ji sanarwar.

Kungiyar kwallon kafar kasar ta Masar EFA, ta ce Salah dan shekara 28, zai sake yin wasu gwaje-gwaje, “cikin sa’o’i masu zuwa.”