Mohamed Salah Na Liverpool Ya Kafa Tarihi A Firimiya Lig

Dan wasan gaba na gefe na kungiyar kwallon Kafa ta Liverpool Mohamed Salah ya Kafa tarihi a bangaren Firimiya lig na kasar Ingila inda ya kasance dan wasan da yafi kowane dan wasa jefa kwallo da kafar hagu a cikin kakar wasa a bangaren Firimiya lig na Ingila.

Matashin dan wasan ya zurara kwallaye har guda ashirin a wasannin Firimiya lig na bana, duk da kafar hagu.

Mohamed Salah, ya jefa kwallonsa wadda ta cika ta 20 da kafar hagu ne a wasan da kungiyar ta lallasa Westham daci 4-1 a gasar Firimiya lig mako na 28 ranar Asabar da ta gabata.

Dan wasan yanzu haka shine dan wasa na biyu a cikin jerin sunayen wadanda suka zurara kwallaye a wasannin fitimiyar bana inda ya jefa kwallaye har 23 a bangaren Firimiya lig na Ingila.

Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, na samansa inda shi kuma ya jefa kwallaye ashirin da hudu a gasar.

Your browser doesn’t support HTML5

Mohamed Salah Na Liverpool Ya Kafa Tarihi A Firimiya Lig