MOGADISHU-Mutane Sha Biyar Sun Mutu A Tagwayen Hare-Hare

Harin kunar bakin wake kusa da fadar shugaban kasa

An kashe sama da mutane goma sha biyar, sama da ishirin kuma suka ji raunuka a wadansu tagwayen hare hare da aka kai yau asabar a harabar ma’aikatun harkokin cikin gida da kuma na tsaro a Mogadishu babban birnin kasar, bisa ga cewar shaidu

An kai harin farko ne lokacin da ‘yan bindiga suka tada manyan nakiyoyi a kofar shiga ma’aikatar harkokin cikin gida kafin wadansu mahara uku suka kutsa ciki. An ga hayaki ya turnuke wurin.

Shaidu sun ce jami’an tsaro sun kai harin yaki da ta’addanci suka yi musayar wuta na sa’oi da dama da maharan kafin suka kawo karshen mamayar suka kuma kashe dukan maharan uku.

Bisa ga cewar shaidu, ma’aikatan gwamnati suna daga cikin wadanda aka kashe a harin na farko, yayinda wani jami’I da ya nemi a saya sunansa yace mai yiwuwa adadin wadanda suka rasu ya karu, yayinda jami’ai suke ci gaba da bincike cikin ma’aikatar, da harabar da kuma ofishin ‘yan sanda dake tsallaken titi.

Mutane da dama sun makale a cikin ma’aikatar lokacin da ake musayar wutar,wadansu kuma suka rika tsalle ta taga suna gudu.

Ma’aikatar dake kan wata hanya da ake yawan hada hada, tana kusa da majalisar dokoki da kuma fadar shugaban kasa.

An kuma kai hari na biyu a harabar rundunar yan sanda dake fuskantar ma’aikatar harkokin cikin gida.

Abdulkadir Abdirahman Aden, shugaban ma’aikatar agajin gaggawa yace tawagarsa ta kwashe sama da mutane goma sha bakwai da suka ji raunuka daga kusa da inda aka kai hare haren.

Kungiyar ta’adda a Somalia Al-Shabab ta dauki alhakin hare haren. Kawo yanzu gwamnati bata yi wani bayani dangane da hare haren da aka yi asarar rayuka ba.