Kasar India ta musanta rade-radin da ake yadawa cewar ta bukaci shugaban Amurka Donald Trump, ya shiga cikin dadaddiya takaddama dake tsakanin kasar da Pakistan akan yankin nan na Kashmir.
“Babu wani roko mai kama da hakan,” a cewar wani jami’i maimagana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Raveesh Kumar, wanda ya rubuta a shafinsa na Tweeter.
Yace duk wata tattaunawa da ya kamata a yi tsakanin India da Pakistan, ana yinta ne kai tsaye a tsakaninsu.
A jiya Litinin ne dai shugaba Trump ya furta cewar Firai ministan India Narendra Modi, ya roke shi da ya shiga tsakanin kasashen biyu akan rikicin yankin Kashmir.
“Idan akwai hanyar da zan taimaka, ina farin cikin zama mai shiga tsakani don a dai-daita.” Trump ya bayyana haka jiya Litinin a fadarsa ta White House, lokacin ganawarsa da Firai ministan Pakistan Imran Khan.