Tsohon gwamnan jihar Massachussetts Mitt Romney ya lashe zaben share fage na jam’iyar Republican da aka gudanar a jihar Nevada jiya asabar, abinda ya kara tabbatar da shi a matsayin wanda ke kan gaba a jerin wadanda ke neman jam’iyar ta tsaida su takarar shugaban kasa, da zai kalubalanci shugaba Barack Obama, a zaben da za a gudanar cikin watan Nuwamba.
A jawabinshi bayan tabbatar da shi a matsayin wanda ya yi nasara, Romney bai yi wata wata ba wajen zargin cewa, Mr. Obama ya juwaya mutanen Nevada baya, jihar da tafi kowacce fama da komadar tattalin arziki.
Romney ya sami sama da kashi arba’in bisa dari na kuri’un da aka kada inda ya kusan ruba kuri’un da abokin takararshi na kuskusa tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Newt Ginngrich ya samu wanda ya zo na biyu, dan majalisa mai wakiltar jihar Texas Ron Paul na biye, yayinda tsohon dan majalisar dattijai Rick Santorum na jihar Pennsylvania ya zo na hudu.
Gingrich ya ci alwashin ci gaba da takara har lokacin da jam’iyar zata yi taronta na kasa domin tsaida dan takara a watan Agusta.