Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rick Santorum ya lashe zaben fidda dan takara a jihohi uku


Rick Santorum, mai neman takarar shugaban kasar a jam'iyar Republican
Rick Santorum, mai neman takarar shugaban kasar a jam'iyar Republican

Mai neman jam'iyar Republci ta tsaida shi takarar shugaban kasa Rick Santorum ya sami gagarimar nasara a jiohohi uku jiya

Yakin neman zama dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar Republican da Rick Santorum ke yi ya sami gagarimin karfin gwiwa a jiya Talata bayan nasarar da ya yi a Minnesota da Missouri da kuma Colorado.

Bayan an tattara yawancin kuri’un, sakamakon ya nuna cewa tsohon dan Majalisar Dattawan Amurka daga Pennsylvania din yace muhimman kuri’un Minnesota da 45%, shi kuma dan Majalisar Wakilai Ron Paul ya zo na biyu da 27% , sai shi kuma tsohon gwamnan Massachusetts Mitt Romney, wanda aka dauka shi ne na gaba-gaba a ‘yan takarar Republcan, ya zo na uku kuma can baya ma da kuri’u 17%.

A zaben Missouri, bayan da aka kusa kammala kidaya, Satorum ya sami kashi 45%, Romney ya zo na biyu da 25%; sannan shi kuma Paul ya zo na uku da 12%.

A jawabin da ya biyo bayan nasarar da ya yi da yammacin jiya Talata a Missouri, Santorum ya yi shelar cewa “har yanzu akawi ra’ayin mazan jiya a Missouri da Minnesota muraran.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG