Minnesota Ta Gabatar Da Korafi Kan 'Yan Sandan Minneapolis

Was masu zanga-zanga kan mutuwar George Floyd

Jihar Minnesota da ke Amurka ta rubuta korafin keta hakkin bil’adama akan rundunar ‘yan sandan birnin Minneapolis game da kisan George Floyd wanda ya mutu bayan da wani dan sanda ya danne wuyansa da gwiwa na tsawon wasu mintoci.

Gwamna Tim Walz da kuma hukumar kare hakkokin bil’adama ta Minnesota ne suka sanar da tura korafin a wani taron manema labarai da aka yi jiya Talata da rana.

Bidiyon da ya nuna mutuwar Floyd da wani ya dauka, wanda ya bazu ko ina ya haddasa zanga-zanga a fadin duniya.

An kori Jami’in dan sandan Derek Chauvin daga aiki kuma ana tuhumar shi da laifin kisan kai a mataki na uku.

Haka kuma an kori wasu jami’an ‘yan sanda su uku da ke da hannu a lamarin amma ba a tuhume su da wani laifi ba.