Jiya Alhamis, ministocin tsaro na kasashe dake kungiyar tsaro ta NATO suka bayyana wasu sabbin shirye shirye na fada da kai daukin soja, yadda zasu iya tura bataliya 30, da jiragen yaki 30, da jiragen yaki na ruwa masu dakon jiragen yaki na sama cikin kwanaki 30 zuwa ko ina a fadin turai inda ake rikici.
Babu cikakken bayani kan daftarin shirin da Amurka ta bayar,kodashike ministocin tsaron kasashen suka ce suna fatar ganin shirin ya fara aiki nan da shekara ta 2020.
Shugabannin kungiyar sun ajiye gefe daya banbance banbance dake akwai tsakain 'yayanta wajen ganin cewa sun karfafa rundunonin su wajen tunkarar kutse ko takala daga Rasha.