Ministocin Tsaro, Harkokin Wajen ECOWAS Na Taro Domin Magance Matsalar Tsaro

Shugaban hukumar kula da kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya bayyana damuwa game da cewar a daidai lokacin da kungiyar ke shirye-shiryen fara shagulgulan bikin cikarta shekaru 50 da kafuwa, mambobinta guda 3 sun bayyana aniyarsu ta ficewa daga cikinta.

Ministocin harkokin waje dana tsaron kasashen kungiyar ecowas, ta bunkasa tattalin arzikin Afrika ta yamma na halartar karo na 53 na taron kwamitin tsaro da sasantawar kungiyar a Najeriya, a matakin ministoci.

Taron na gudana ne a shelkwatar hukumar kula da kungiyar Ecowas dake birnin Abuja.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Jakada Yusuf Tuggar ne ke jagorantar karo na 53 na taron kwamitin tsaro da sasantawar kungiyar ecowas din.

A jawabinsa na maraba, shugaban hukumar kula da ECOWAS, Omar Touray, ya bayyana damuwa game da cewar a daidai lokacin da kungiyar ke shirye-shiryen fara shagulgulan bikin cikarta shekaru 50 da kafuwa, mambobinta guda 3 sun bayyana aniyarsu ta ficewa daga cikinta.

Touray ya bukaci kasashe mambobin kungiyar su sake jaddada muradun ECOWAS.

Ya kara da cewar taron zai tattauna a kan batutuwan da suka shafi yanayin siyasa da tsaro da kuma harkokin bada agaji da yankin na yammacin Afrika ke ciki, tare da kafa kotun musamman a kan tauye hakkin dan adam.