Jami’ai a taron da ministocin suka gudanar a Brussel a jiya Talata, sun ce daga cikin matakan da ake dubawa, har da batun tura karin jiragen ruwan yaki a tekun Meditareniya da jiragen sama na yaki a filin jirage da ke Incirlik, da kuma bunkasa makamai masu linzami.
Har ila yau ministocin sun kwatanta abinda ke faruwa a iyakar Turkiyya da Syria, a matsayin wani lamari mara tabbas, suna masu jaddada za su ci gaba da samar da matakan kariya ga duk wata kasa da ta kasance mamba a kungiyar ta NATO.
Sakatare Janar na kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg, ya ce duk mambobin kungiyar su yi shawara nan da ‘yan makwanni masu zuwa game da irin taimakon da za su baiwa Turkiyya
Ministan harkokin wajen Lithuania, Linas Linkevicius, ya ce, ya kamata a baiwa Turkiyya duk irin taimakon da ta nema, yana mai karfafa cewa duk wani abu da ke barazana ga kasa daya, yana baraza ne ga kungiyar ta NATO.