Da take zantawa da manema labarai, Ministar ta bayyana cewa, ma’aikatar ta tare da hadin gwiwar Kakakin Majalisar Dokokin jihar Neja, da kuma sarakunan gargajiya daga jihar, a halin yanzu suna gudanar da bincike kan shekarun ‘yan matan domin sanin ko sun kai shekarun da aka kayyade na aure.
A cewarta, a yanzu ma’aikatar harkokin mata za ta mayar da hankali wajen tallafawa ‘yan mata, da ma sauran wadanda rashin tsaro ya shafa a jihar.
A makon da ya gabata ne Shugaban Majalisar jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, ya bayyana shirin aurar da marayu 100 a mazabarsa a wani mataki na rage radadin da suke ciki.
Yayin da ake ci gaba da cece-ku-ce a kasar akan lamarin, Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC), ta bukaci Ministar da ta janye karar da ta rubutawa babban sufeton rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Shugaban kungiyar MURIC reshen jihar Kano, Malam Hassan Indabawa, wanda ya yi wannan kiran a daren ranar Alhamis cikin wata sanarwa, ya bukaci ‘yan Najeriya da su koyi mutunta al’adun juna.