Ministan tsaro Janar Mansur Dan Ali mai ritaya ne ya bayyana haka a Minna lokacin da ya isa jihar Neja domin bude wata sabuwar gada da gwamnatimn Najeriya ta gina a kauyen Sabon garin Sarko dake yankin karamar hukumar Magama.
Ministan ya bayana cewa, shugaba Buhari ya damu da wannan matsala, shiyasa gwamnatin sa ta dukufa wajen gina kwalbatoci da samar da gadoji a sassan Najeriyar, ya kuma kara da cewa wannan aiki na daya daga cikin ayyukan shawo kan matsalar zaizayar kasa guda 18 da ya samu amincewar shugaban kasa a yankuna 6 na siyasar najeriya, domin magance wannan matsala ta zaizayar kasa da kuma ambaliyar ruwa.
Dan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin Rijau da Magama, Shehu Slow ne ya jagoranci aikin samar da gadar inda ya ce an kashe sama da miliyan 100 wajen gudanar wa wannan aikin.
Saurari Cikakken Rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Your browser doesn’t support HTML5