Ministan Shari’a Ya Ce Za Su Jira Atiku Ya Je Kotu Don Su Kare Kansu

ABUJA: Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar

Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami ya ce hanya mafi a’ala ga abokan hamaiya da ba su amince da sakamakon zabe ba shi ne tafiya kotu.

Malami na magana ne daidai lokacin da dan takarar babbar jam’iyyar adawa Atiku Abubakar, ya yi watsi da sakamakon zaben da baiyana cewa shi da abokan tafiyar sa za su sanar da matakin da za su dauka na gaba.

In za a tuna Atiku dai da ya yi magana a taron manema labaru, ya yi alwashin karbo abun da ya zaiyana da hakkinsa.

Minista Malami wanda shi ne mai ba da shawara kan shari’a a tsohuwar jam’iyyar Buhari CPC, ya ce zuwa kotu ba sabon abu ba ne.

Da ya ke sharhi kan zaben shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci duk wadanda ba su samu nasara ba su rungumi kaddara.

Da alamu dai musayar bakaken maganganu tsakanin magoya bayan ‘yan siyasa sun yi sauki a wannan karo ba kamar yadda ya faru a 2015 da 2011 ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Shari’a Ya Ce Za Su Jira Atiku Ya Je Kotu Don Su Kare Kansu - 3'00"