Ministan Matasa Da Wasanni Ya Kafa Kwamitin Sulhu A Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya

Sakamakon rikece-rikicen da ake samu a cikin hukumar kula da kwallon kafa ta tarayyar Najeriya, NFF na shugabanci tsakanin bangaren Chris Giwa da kuma Amaju Pinnick.

Ministan matasa da wasanni na Najeriya, Batista Solomon Dalung, ya nada kwamitin dattawa masu ruwa da tsaki a bangaren kwallon kafa su shida domin kawo karshen rikice-rikicen.

Tsohon Shugaban Hukumar NFF, Abdulmumini Aminu, zai jagoranci kwamitin sulhu na dattawa mai dauke da mutane 6 don tabbatar da zaman lafiya a cikin hukumar kwallon kafa na Najeriya.

Da yake rantsarda kwamitin, ministan wasanni Solomon Dalung, ya ce ya lura cewa rikicin da ake fama da shi a NFF ya hana samun cigaba da bunkasa kwallon kafa a Najeriya.

Kwamitin, wanda aka ba shi makonni biyu don mika rahotonsa, ya kunshi tsohon shugaban kungiyar NFF, Col Abdulmumini Aminu a matsayin shugabanta. Sauran mambobi sun hada tsohon shugaban NFF, Alhaji Ibrahim Galadima, da Anthony Kojo Williams, Farfesa Onye Gyd - Wado, Dr. Sam Sam Jaja da kuma Mr. Bolaji Ojo - Oba.

Akwai wadanda zasu kasance a matsayin masu tattara bayannan kwamintin wato sakatarorinta wanda suka hada da Danjuma Muhammed, mai rikon kwarya na Sakatare Stanley Okebugwu, sai kuma Reuben Tiyatiye.

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Matasa Da Wasannin Ya Kafa Kwamitin Sulhu A Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeria