Ministan babban birnin tarayya Abuja Bala Mohammed ya ci alwashin korar shan inna a kasar yayinda ake ci gaba da fuskantar kalubala kasancewarta daya daga cikin kasashe hudu rak a duniya da ake ci gaba da samun yaduwar cutar.
Ministan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da yaki da cutar matakin karshe a birnin tarayya Abuja. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayyar ta ba gwamnatocin jihohi damar gudanar da yaki da cutar yadda suka ga dama ba tare da tsangwama ba domin ganin nasarar shirin.
Saneta Bala Mohammed ya kuma yabawa kungiyoyi masu zaman kansu da kuma ma’aikatan jinya a matakai dabam dabam, domin goyon bayan da suke badawa ga nasarar shirin. Yayinda ya yi kira ga iyaye mata su bada hadin kai ta wajen fito da ‘ya’yansu a yi masu rigakafin.
A nashi jawabin, sarkin Juwa Alhaji Idris Isa ya bayyana muhimmancin hada hannu wajen yakar cutar, kasancewa an fara nunawa Najeriya kyama domin ci gaba da yaduwar cutar ganin yadda ake tilas hana ‘yan Najeriya shiga wadansu kasashe sai an diga masu maganin shan inna kafin kyale su su shiga.
Iyaye mata da suka halarci gangamin sun koka dangane da talauci da ake fama da shi. Suka kuma yi kira ga gwamnati ta samar da ayyukan yi musamman ga matasa da suke zaman kashe wando.