Magoya bayan kungiyar kwallon kafar Manchester United ta Ingila na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan matakin da kungiyar ta dauka na sallamar mai horar da ‘yan wasanta Ole Gunnar Solskjaer.
United din ta ba da sanarwar sallamar locin ne a jiya Lahadi, kwana daya bayan da kungiyar ta sha dan karen kashi a hannun Watford da ci 4-1 a wasan gasar Premier.
Wasan dai na daga cikin wasanni 3 da suke zaman ma’auni na damar karshe da kungiyar ta baiwa kocin sakamakon koma baya da take samu, a yayin da magoya bayan kungiyar suka yi ta kiran da a sauya kocin.
Umar Faruk Bukkuyum, daya ne daga cikin magoya bayan kungiyar ta Manchester United a Najeriya, ya kuma bayyana cewa akasarin magoya bayan kungiyar sun ji dadi tare da yin na'am da matakin kungiyar.
To sai dai kuma yana ganin cewa da sauran rina a kaba, musamman la'akari da wanda aka baiwa rikon kwarya na shugabancin kungiyar, a yayin da kuma ake ganin ba kowa ne zai iya daukaka kungiyar ba.
A halin da ake ciki kuma wasu rahotanni na bayyana cewa kungiyar ta Manchester United ta tuntubi tsohon mai horar da ‘yan wasan Real Madrid ta kasar Spain, Zinadine Zidane, domin ya maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer.
To sai dai wata majiya da ke kusa da kocin dan kasar Faransa, ta ce bai da sha’awar karbar aikin na United a halin yanzu, duk kuwa da cewa yanzu haka yana zaune ne ba aiki.
Zidane ya bar kungiyar ta Real Madrid karo na farko a shekarar 2018, to amma ya koma kungiyar bayan shekara 1, kana kuma ya bar ta karo na 2 a watan Mayun wannan shekara.
Ya sami lashe gasar zakarun Turai har sau 3 a jere da kungiyar daga shekarar 2016, inda bayan komawarsa ta 2 kuma ya lashe gasannin La Liga da Super Cup na kasar.
An ta’allaka Zidane da komawa kungiyar PSG ta kasar Faransa, kuma majiyar ta bayyana cewa ya fi sha’awar tafiya kungiyar idan damar hakan ta samu.
A bangare daya kuma rahotannin sun bayyana cewa kocin PSG Mauricio Pochettino, ya bayyana cewa a shirye yake ya bar PSG din zuwa Ingila, idan har Manchester United ta neme shi.
Ole Gunnar Solskjaer
Your browser doesn’t support HTML5