Hakan na faruwa ne lokacin da wasu iyaye da dalibai ke ganin ya kamata gwamnati ta kula da matsalolin da ke tarnaki ga karatu.
Mafi yawan yaran da basa samun damar zuwa makaranta a Najeriya, suna yankin Arewa, abin da ya sa ake kallon yankin a zaman wanda da bai ci gaba ba a harkar ilimi.
To sai dai gwamnatoci a yankin sun mayar da himma wajen sauya wannan lamari, inda suke hada hannu da hukumomin dake bayar da tallafi na Duniya don ganin an saka yara a makaranta.
A jihar Sokoto, baya ga shirye-shiryen bunkasa ilimi da gwamnatin ke cewa tana aiwatar wa, haka kuma ta hada hannu da bankin Duniya wajen mayar da dubban daruruwan yara makaranta karkashin shirin samar da ilimi ga kowa.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya ce gwamnati ta kudurci yin aiki tukuru domin samun nasarar shirin.
Sai dai wasu dalibai da iyaye sun koka ganin cewa daliban da suka kammala makarantun sakandare tun shekarar 2019 har yanzu basu samu sakamakon jarabawar su ta NECO ba, koda za su iya samun gurabun karatu a makarantu na gaba, suna zaune gida har ga daliban shekara ta 2020 sun bi sahun su.
kwamishinan ilimi na jihar, Muhammad Bello Abubakar ya ce hakan ta faru ne saboda bashin da hukumomin shirya jarabawar WAEC da NECO suke bin gwamnati, na sama da Naira miliyan dubu, amma dai sun tattauna da hukumomin har WAEC ta fitar da nata sakamakon, amma har yanzu suna fama da NECO.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5