Yayin da ake shirin kammala taron da ke dubi kan inda ake a yakin da ake yi cutar kanjamau ko kuma AIDS/SIDA a birnin Durban na Afrika ta Kudu a yau Juma’a, masana na shakkun ko za a iya shawo kan cutar nan da shekarar 2030.
WASHINGTON D.C. —
Domin a cewarsu akwai miliyoyin mutane da ba sa samun maganin makarin wannan cuta wacce ta fi yawa a kasashen masu tasowa musamman a Nahiyar Afrika.
A cewar masanan, hukumomi ba sa maida cikakken hankali wajen yaki da cutar mai haddasa AIDS.
Sai dai kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce sun dukufa wajen ganin an samu maganin cutar a duk fadin duniya.
Hajiya Maimuna Muhammed, tsohuwar mai shirya tsare-tsare ce a kungiyar NACA mai yaki da bazuwar cutar a Najeriya.
Jummai Ali ta tambaye ta shin za a yi nasarar kawar da wannan cuta kuwa?
Saurari wannan
Your browser doesn’t support HTML5