Mikel mai shekaru 33, zai koma kungiyar Stoke City da ke fafata gasar Championship, inda zai kasance dan wasa na 4 da kungiyar ta cefano a wannan bazara.
Manajan kungiyar Michael O’Neill ya bayyana farin cikin samun dan wasan, bayan kammala tattaunawa da kuma cimma matsaya da shi, inda dan wasan ya nuna bukatarsa na dawowa fafata gasar Premier, wanda kuma ya ke fatan yiwuwar hakan a kungiyar ta Stoke City.
Mikel ya kwashe tsawo shekaru kusan 11 a kungiyar Chelsea, inda buga mata wasanni fiye da 370, ya kuma sami nasarar lashe gasannin Premier, FA Cup, Europa League da kuma gasar Zakarun Turai.
Ya bar Chelsea zuwa kungiyar Tianjin Teda ta kasar China inda ya yi zama na dan lokaci, kana ya sake komawa Ingila a kungiyar Middlesbrough, kafin ya koma Trab-zons-por ta kasar Turkiyya.
Kwantaragin Mikel ya kai karshe ne sakamakon takaddama da ta barke tsakaninsa da shugabannin kungiyar a farkon somawar annobar coronavirus.
A matakin kasa kuwa, Mikel ya bugawa kasarsa ta Najeria wasa har sau 91, inda ya sami lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2013, ya kuma lashe lambar tagulla a gasar wasanni Olympics ta Rio a shekarar 2016.