Gwamnan jihar Michigan, Grechen Whitmer ta ce jihar za ta dauki duk wani mataki na shari’a a kan daya daga cikin masu madatsun ruwan da suka fashe a farkon makwannan, da ya haifar da ambaliya sosai a wasu yankuna da dama.
An kwashe sama da mazauna yankin dubu 10,000 a tsakiyar garin Midland a ranar Laraba, yayin da kogin Tittabawassee ya yi ambaliya sa’o’i bayan da madatsar ruwa ta Edenville, da take a kilomita 32 a arewa, ta fashe bayan shafe kwanaki ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Jami’ai sun ce Kogin Tittabawassee ya haura da mita 10 a yammacin ranar Laraba kafin ya matsa baya daga yankuna da dama.
Gagarumin kwashe jama’ar yana da rikitarwar saboda barazanar COVID-19 a yankin. Duk da yake karamar hukumar Midland ta tabbatar da mutane 80 sun kamu da wadanda suka mutu 10, Jahar Michigan ta bada rahoton wadanda aka tabbatar sun kamu mutum dubu 52,350.