Trump ya sanya hannu a umarni kan bakin haure a lokacin da ya kai ziyara a ma’aikatar tsaron cikin gida, hukumar tarayya dake da alhakin kare iyakokin Amurka.
Trump ya shaidawa tashar talabijin ABC News cewa, nan da watanni masu zuwa za a fara gina katangar kuma ya ci gaba da jaddada cewa, kasar Mexica ce zata biya kudin gina katangar.
Yace, za a bi wani irin tsari ne, ya yiwu tsari mai sarkarkiya. Kuma yakamata ku fahimci cewar wannan abin da nake yi zai taimakawa Amurka, kazalika zai taimakawa Mexico. Muna son mu tabbatar da daidaito da karfafa al’amura a Mexico.
A wani sakonsa ga al’ummar kasar Mexico a jiya Laraba, shugaba Enrique Pena Neito ya sake jaddada matsayansa cewar kasarsa ba zata dauki nauyin gina katangar ba.
Idan akwai inda wani dan Mexico dake zaman ci rani ya fada cikin matsala yana bukatar taimako, inda zamu kasance ke nan, wurinda ya kamata kasar ta maida hankali ke nan.
Ina bakin ciki da kuma nuna rashin amincewa da shawarar da Amurka ta yanke na cigaba da gina Katanga, da shekara da shekaru, a maimakon ta hada kawunanmu, take raba mu. Mexico bata yarda da katanga ba.