Ana fargabar cewa, masana’antar harkokin sadarwa ta miliyan dubu dari da hamsin na kasar India, da ke dogara ga kasuwannin Amurka, na iya fuskantar koma baya, kasuwarta kuma fadi idan gwamnatin Trump ta kara tsaurin dokokin daukar kwararrun ma’aikata daga kasashen ketare.
Farkon wannan watan, aka gabatar da wani kuduri a majalisar dokokin Amurka ta kara matsakaicin karancin albashi ga guraban da ake ba takardar izinin aiki A Amurka H-1B, daga dala dubu sittin zuwa dubu dari a shekara.
Kamfanonin fasahar sadarwa ta zamani, dake aikawa da daruruwan kwararrun ma’aikata a wannan fannin Amurka, sune suka fi cin moriyar takardar bisa ta H-1B, dake ba kwararru damar yin aiki a Amurka.
Wadanda suka gabatar da kudurin sunce zai taimaka wajen cike gibi da ya shafi tsarin shige da fice da kamfanoni ke amfani da shi wajen shigo da ma’aikata masu arha daga kasashen ketare.